A yau komitin nazarin makomar Iraqi zai mika rahotonsa | Labarai | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau komitin nazarin makomar Iraqi zai mika rahotonsa

A yau ake sa ran mika rahoton komitin nazari game da makomar Iraqi.

Majiyoyi daga CNN sunce rahoton yayi kira ga Amurka da ta canza rawa da sojojinta ke takawa a kasar Iraqi daga fagen daga zuwa ga masu bada taimako ga sake gina kasar ta Iraqi.

Rahoton komitin karkashin jagorancin tsohon sakataren harkokin wajen Amurka James Baker,wanda zaa mikawa shugaba Bush nan gaba a yau din nan ya kuma bada shawarar tsara hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya.