A yau Jamusawan da aka sako a Iraki ke dawowa gida | Labarai | DW | 03.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau Jamusawan da aka sako a Iraki ke dawowa gida

A yau larabawa Jamusawan nan biyu, wadanda aka sako jiya bayan an yi garkuwa da su a Iraqi kimanin makonni 13 da suka wuce, zasu iso gida Jamus. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier wanda a halin yanzu yake wata ziyara a Chile, ya ce yayi magana da mutanen biyu wadanda aka sako su ba tare da an yi musu rauni ba. Sai dai har yanzu ba´a bayyana hanyoyin da aka bi aka sako su ba. A lokacin da take magana da manema labarai, SGJ Angela Merkel ta nuna farin cikin ta da jin wannan bushara inda ta mika sakon fatan alheri da kuma godiyarta ga iyalai da sauran al´umar wannan kasa da cewa ba su manta da mutanen biyu ba. A ranar 24 ga watan janeru wasu ´yan bindiga a garin Baiji dake arewacin Iraqi, suka yi garkuwa da Thomas Nitzschke da rene Bräunlich dukkansu daga garin Leipzig. Sun yi ta barazanar kashe su idan ba´a biya musu bukatunsu ba.