A yau aski ya kai gaban goshi na fara aikin Hajjin bana | Labarai | DW | 28.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau aski ya kai gaban goshi na fara aikin Hajjin bana

A daidai lokacin da shirye shiryen fara aikin hajjin bana suka kankama, a yau ake sa ran isar musulmi kimanin miliyan biyu daga ko-ina cikin duniya a birnin Makka. A halin da ake ciki mahajjata sama da miliyan 2 sun hallara a Mina dake kusa da birnin na Makka. A cikin matakan da take dauka don dakile ayyukan ta´adda da masu shirin kai hari ko hana aukuwar turmutsutsu a tsakanin mahajjata, a bana ma hukumomin Saudiyya sun tsaurara matakan tsaro musamman a birnin na Makka. A bara akalla mutane 360 suka rasa rayukansu a wata turereniya da aka yi a lokacin aikin hajji. A ranar litinin mai zuwa za´a kammala aikin hajjin na bana.