A yau ake shagugulan karamar Sallah a kasashen Larabawa | Labarai | DW | 23.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ake shagugulan karamar Sallah a kasashen Larabawa

Bayan da a jiya musulmi a wasu kasashe kamar Nijeriya da janhuriyar Nijer suka yi bukin karamar Sallah, a yau litinin daukacin kasashen musulmi na yankin Golf da na larabawa ke ta su sallar idin, bayan kammala azumin watan ramalana. Hukumomin kula da sha´anin addini a kasashen Saudiya, Bahraimn, Kuwaiti, Qatar da haddaiyar daular Larabawa da na yankunan Falasdinawa sun sanar da cewa a yau suke fara shagulgulan karamar salla. Wata sanarwa da ta fito daga wata kungiya mai alaka da Al-Qaida wadda ta yi shailar kafa shari´ar musulunci a Iraqi ita ma ta ce a yau take bukin Eidel Fitr. Kamar a kowace shekara a bana ma an samu bambamci ra´ayi game da takamaime ranar ajiye azumin na watan ramalana. Yayin da a wasu kasashe aka yi kwanaki 29 a wasu kuwa kwana 30 aka yi ana wannan ibada mai alfarma.