A yau ake san ran kasashen turai zasu kara matsawa Iran lamba kan tayi da sukayi mata | Labarai | DW | 11.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ake san ran kasashen turai zasu kara matsawa Iran lamba kan tayi da sukayi mata

A yau en ake sa ran Kungiyar Taraiyar Turai zata ci gaba da matsawa kasar Iran lamba domin ta gaggauta bada amsa game da tayin da kungiyar tayi mata.

Sakataren harkokin wajen kungiyar javier Solana zai gana da wakilin Iran Ali Larijani yau a birnin Brussells tare kuma da wakilan kasashen Burtaniya da Faransa da Jamus da kuma Rasha.

Iran dai a nata bangare tace zata bukaci karin haske ne game da wasu abubuwa da suka shuge mata duhu cikin wannan ihasani a ganawar ta yau.

Kasashen yammacin duniya dai sun bukaci Iran ta mika amsarata kafin taron kungiyar kasashe 8 masu arzikin masanaatanu da zaayi mako mai zuwa a birnin St.Petersburg,Iran din dai ta hakikance sai a ranar 22 ga watan Agusta ne zata bada nata amsa game da tayin da akai mata.