1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau ake sa ran takunkumin Ivory Coast zai fara aiki

Hauwa Abubakar AjejeFebruary 7, 2006

Wadanda suka jagoranci zanga zangar kin jinin Majalisar Dinkin Duniya na watan daya gabata a Ivory Coast,sunyi watsi da batun lakaba musu takunkumi da ake sa ran yau zai fara aiki ,suna masu cewa,wannan mataki ba zai dakatar da zanga zanga akan titunan kasar ba.

https://p.dw.com/p/Bu1p
Hoto: AP

Shugabannin matasa,Charles Ble Goude da Eugene Djue,da suke tsananin goyon bayan shugaba Laurent Gbagbo,suna fuskantar haramcin zirga zirga da kuma dakatar da kadarorinsu,bayan magoya bayansu sun yi ta jifa tare da jefa bama baman fetur akan gine gine Majalisar Dinkin Duniya a lokacin zanga zanga na watan daya gabata.

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dai,ya amince da lakaba takunkumi akan duk wani wanda yake hana ruwa gudu a kokarin sake hadewar kasar data rabe gida biyu,tun yar gajeruwar yakin basasa a 2002-3,kodayake baa kaddamar da takunkumin ba.

Amma karkashin shawarar kasashe 4,a yau talata takunkumin zai fara aiki kan Ble Goude,Djue da komandan yan tawaye da ake zargi da take hakkin bil adama,sai dai idan daya daga cikin membobin komitin sulhun bai goyi bayan takunkumin ba.

Wasu kuma suna ganin cewa,wannan takunkumi zai kara hura wutar tashe tashen hankula ne a kasar.

Shi dai Ble Goude ya fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa,shi fa baya tsoron wannan takunkumi,ya kuma bukaci magoya bayansa da kada su ce zasu maida martani da zarar takunkumin ya fara aiki.

Ble Goude da Djue,suna zargin masu shiga tsakani na kasa da kasa da tsoma baki a harkokin kasar Ivory Coast mai yancin kanta,karkashin shirin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya,wadda karkashinsa ake sa ran gudanar da zabe a watan oktoba mai zuwa.

Dukkanninsu biyu,Bled a Djue,sun fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa,basu da asusu a bankuna da zaa iya dakatarwa,hakazalika Djue yace bai damu ba a haramta masa tafiye tafiye.

Amma a garin Korhongo da yan tawaye suke rike da shi a arewacin kasar,daruruwan mutane sun hallara a wajen ofishin Majalisar Dinkin Duniya a jiya litinin suna masu bukatar majalisar ta janye batun lakaba takunkumin akan wani komandan yan tawayen,Fofie Koukou,wanda ake zargi da take hakkin bil adama.

Zanga zanga na watan daya gabata,ya girgiza dakarun Majalisar Dinkin Duniya su 7,000,inda suka bar sansanoninsu dake yammacin kasar,bayan sun harbe har lahira wasu masu zanga zanga 5,wadanda suke kokarin sace makamai da ababen hawa a sansanin.

Akwai kuma dakarun kasar Faransa 4,000 dake marawa dakarun na Majalisar Dinkin Duniya baya.

A jiya litinin ne dai kuma komitin sulhu,ya amince da kaiwa wasu dakarun majalisar 200 daga Liberia zuwa Ivory Coast,domin su kara marawa yan uwansu baya.

Sai dai jamian diplomasiya daga komitin sulhun,sunce Amurka ta datse bukatar da sakatare janar Kofi Annan ya mika ta aikewa da Karin yan sanda zuwa Ivory Coast,tana mai ja da cewa,kara yawan dakarun Majalisar Dinkin Duniya ba shine zai kawo zaman lafiya a kasar ba,muddin dai dukkan bangarori da abin ya shafa,basu da zummar yin hakan.