A yau ake rantsar da shugabar Liberia | Labarai | DW | 16.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ake rantsar da shugabar Liberia

A yau ne ake rantsar Ellen Johnson Sir-Leaf,a matsayin shugabar kasar Liberia,mace ta farko zababbiyar shugaba kasa nahiyar Afrika.

Manyan jamian kasashen Afrika da na ketare ake sa ran zasu halarci bikin na yau a birnin Monrovia,ciki kuwa har da uwargidar shugaba Bush na Amurka Laura Bush da ministan harkokin wajen kasar Sin Li Zhaoxing.

Ellen ce ta lashe zaben shugaban kasar Liberia da aka gudanar a watan nuwamba daya gabata.

Masu lura da alamura sunce aiki tukuru dake gabanta,na sake gina kasar Liberia bayan yakin basasa da aka kawo karshensa a 2003 ,zai dogara ne akan taimako na kasa da kasa.

Ita dai Ellen kwararriya a fannin tattalin arziki ta rike matsayin ministar kudi kafin a zabe ta shugaba.