A yau ake jana´izar Walid Eido wanda aka yiwa kisan gilla a Libanon | Labarai | DW | 14.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ake jana´izar Walid Eido wanda aka yiwa kisan gilla a Libanon

Kwamitin sulhun MDD gaba dayansa ya yi tir da harin bam din da aka kai a Libanon. A cikin wata sanarwa da suka bayar, membobin kwamitin sulhun sun yi Allah wadai da kowane irin yunkuri na haddasa rudami a cikin kasar ta Libanon. Suka ce dole ne a kame tare da hukunta wadanda ke da hannu a wannan aika-aika. A harin dai an halaka dan majalisa mai sukar lamirin Syria Walid Eido da kuma wasu mutane 9. A gobe juma´a kungiyar kasashen Larabawa zata yi wani taro na musamman a birnin Alkahira na kasar Masar don tattaunawa akan halin da ake ciki a Libanon da kuma yankunan Falasdinawa. Mahukunta a Libanon sun zargi Syria da hannu a kisan na Walid Eido wanda shi ne mutum na 7 dake adawa da Syria da aka halaka a cikin shekaru 2. FM Fuad Siniora ya ayyana yau alhamis ta zama ranar makoki a kasar baki daya.