A yau ake hawan Arfa | Labarai | DW | 09.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau ake hawan Arfa

Fiye da mahajjata miliyan 2 ne a yau suka dunguma hawar Arfa a kasar mai tsarki na Saudiya domin sauke faralin hajjin bana.

Dubun dubatar mahajjatan sun suna ci gaba da barin Mina zuwa filin arfa inda annabi (SAW)yayi hudubarsa ta ban kwana a shekara ta 632 miladiya.

Kimanin jamian tsaro 60,000 ne da na kiwon lafiya suke cikin shirin ko ta kwana domin yiwuwar turmutsutsu ko wani hari a lokacin aikin hajjin na bana.