1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau ake cika shekaru 20 da tashin gobara a tashar nukiliya ta Chernobyl

April 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0X

A yau kasar Ukraine ke gudanar da bukukuwan cika shekaru 20 da aukuwar hadarin nukiliya mafi muni a duniya a tashar makamashin nukiliya ta Chernobyl. An yi shiru na minti daya tare da kada kararrawar coci don tunawa da daidai lokacin da hadarin ya auku. A daren 26 ga watan afrilun shekara ta 1986 gobara ta tashi a sashe na hudu na tashar makamashin nukiliyar ta Chernobyl. Bindigar da wurin ya yi ta fasa rufin din tashar, abin da ya baza sinadarin nukiliya a sararin samaniyar ilahirin tsohuwar Tarayyar Soviet da ma Turai baki daya. Alkalumman da MDD ta bayar sun nunar da cewa mutane sama da dubu 9 suka mutu sakamakon hadarin da kuma cucuttukan da wannan hadarin ya janyo. To amma wani rahoton da kungiyar kare muhalli ta Green Peace ta fitar a bara ya kiyasce cewa wadanda suka mutun sun kai mutum dubu 93. Har yanzu kuwa ana fama da cucuttuka iri dabam-dabam sakamakon wannan bala´i.