1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau ake bude taron kungiyar taraiyar turai da shugabannin Latin Amurka

May 12, 2006
https://p.dw.com/p/Buyj

Nan gana a yau jumaa ne zaa bude babban taro akan ciniki tsakanin kungiyar taraiyar turai da shugabanin kasashen latin Amurka,a Vienna kasar Austria.

Babban taron na shugabanin kasashe da gwamnatoci 60,zai mayarda hankali ne akan hadin kan ciniki,da batun man fetur da kare hakkin bil adama.

Masu lura da alamura sunce,da kyar ne bangarorin 2 su cimma matsaya akan wata yarjejeniyar hadin kan ciniki,wadda aka kwashe shekaru ana muhawara akai.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zata mika kasida wajen taron na kwanaki 3.