A yau aka cika shekaru 2 da hare-haren ta´addanci a London | Labarai | DW | 07.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A yau aka cika shekaru 2 da hare-haren ta´addanci a London

A yau Birtaniya ta yi bukin cika shekaru biyu da kai hare haren bama-bamai akan tsarin sufurin birnin London. FM Birtaniya Gordon Brown da ministocin gwamnati sun ajiye furanni a tashar jirgin karkashin kasa ta King´s Cross don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a hare hare. A ranar 7 ga watan 7 na shekara ta 2005 wasu ´yan kunar bakin wake su 4 suka kai hari a cikin jiragen karkashin kasa 3 da wata bas, inda suka halaka kan su da kuma mutane 52.