A wannan makon mai karewa, ko da shi ke girgizar kasar da ta wakana a ... | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

A wannan makon mai karewa, ko da shi ke girgizar kasar da ta wakana a ...

kasar Iran ita ce ta fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, amma duk da haka ba su yi watsi da al'amuran nahiyar Afurka ba. Misali jaridar Süddeutsche Zeitung ta gabatar da wani dogon rahoto a game da masu mulke-mulke na kama karya a nahiyar Afurka. Jaridar sai ta ci gaba da cewar: "Wadannan 'yan kama karya na nahiyar Afurka sun zama tamkar wata shaida ce ta kashe-kashen gilla da azabtar da fursinoni da arzuta kai da kai a yayinda talakawan kasa ke cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi a game da makomar rayuwarsu, amma fa duk da haka, bayan sun kawo karshen mulkinsu, babu wani dake kurarin gurfanar da su gaban shari'a domin amsa wadannan danyyun laifuka. a maimakon haka akan ba su wata kariya ne a hukumance, kamar dai tsofon shugaban kasar Kenya Daniel Arap Moi." To sai dai kuma duk da wannan korafi da jaridar tayi ta kuma kara da bayanin cewar a wani lokaci wannan mataki yana da muhimmanci matuka ainun domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasashen da lamarin ya shafa. Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung tayi bitar halin da ake ciki ne a kasar Kenya, shekara daya bayan canjin gwamnatin da aka samu a kasar a cikin ruwan sanyi. Ta ce ko da shi ke maganar fallasa tabargazar cin hanci na jami'an tsofuwar gwamnati ita ce ke mamaye kanun rahotannin kafofin yada labaran Kenya, amma fa ita kanta sabuwar gwamnatin ta Kibaki ba ta tsira ba, inda mutane ke korafi a game da kin gudanar da bincike akan shi kansa tsofon dan kama karya Daniel Arap Moi. Jaridar sai ta kara da bayanin cewar: "Bai zama abu mai sauki ga gwamnatin shugaba Kibaki mai fafutukar tsaftace kasar Kenya da kuma farfado da tattalin arzikinta da ya tabarbare a cikin shekaru gwamman da suka wuce ba, da ta kyale tsofon shugaba Daniel Arap Moi ya ci gaba da zama gabansa gadi. Amma ga alamu ta dauki wannan mataki na barin kaza cikin kashinta ne saboda tabbatar da kwanciyar hankali da hadin kan kasar Kenya tare da mayar da hankalin wajen kyautata makomar wannan kasa dake gabacin Afurka." A farkon wannan makon aka aiwatar da kisan gilla akan jakadan fadar mulki ta Vatikan a kasar Burundi. A lokacin da take tabo wannan batu a cikin rahoton da ta bayar dangane da ci gaban da ake samu a kasar ta kuryar tsakiyar Afurka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi: "Kungiyar tawayen FNL ta kasar Burundi tayi fatali da zargin da ake mata na cewar tana da hannu dumu-dumu a kisan gillar da aka yi wa Archbishop Michael Courtney, jakadan paparoma a kasar tana mai tofin Allah tsine akan masu alhakin wannan danyyen aiki. Akan fuskanci bata kashi tsakanin askarawan gwamnati da dakarun kungiyar akai-akai. A watan mayun da ya gabata an samu kyakkyawan ci gaba inda shugaba Buyoya dan Tutsi ya danka al'amuran mulki a hannun Ndayizaye, dan Hutu dake da rinjayen kashi 80% a kasar, domin biyayya ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin tsofuwar gwamnatin da 'yan tawayen FDD a Arushan Tanzaniya misalin shekaru ukun da suka wuce. To sai dai kuma ita kungiyar FNL ba ta da hannu a wannan yarjejeniya, wacce ke da nufin kawo karshen yakin basasar Burundi da yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu 200 a cikin shekaru goman da suka wuce." A cikin wani rahoton da ta bayar jaridar Süddeutsche Zeitung tayi korafi a game da yadda Nijeriya ta kiya kememe a game da danka tsofon shugaban Liberiya Charles Taylor domin fuskantar shari'a a kotun kasa-da-kasa a Saliyo alhali kuwa yana da hannu dumu-dumu a ta'asar kisan gilla da azabtar da talakawan kasar tare da rufa wa 'yan tawayen RUF baya. Jaridar sai ta kara da cewar: "Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo dake karbar bakuncin Charles Taylor ya ki ya mika tsofon dan kama karyar domin fuskantar shari'a a Freetown. Ana dai yayata rade-radin cewar akwai wata dangantaka ta kut-da-kut tsakanin daya daga cikin 'ya'yan Obasanjo da dangin Charles Taylor kuma hakan na daga cikin dalilan kiyawar da Nijeriya take yi na cafke shi, inda kuma take kashe makudan kudi domin kyautata jin dadin rayuwarsa da mukarrabansa a kasar."