A wannan makon ma rikicin Sudan ya fi daukar hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 07.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

A wannan makon ma rikicin Sudan ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

Mawuyacin hali na zaman dardar da ake ciki a lardin Darfur na yammacin kasar Sudan shi ne jaridun Jamus suka fi mayar da hankali kansa

'yan gudun hijirar Darfur a yammacin Sudan

'yan gudun hijirar Darfur a yammacin Sudan

A wannan makon ma daidai da makon da ya gabata jaridun na Jamus sun fi mayar da hankalinsu ne akan mawuyacin halin da ake ciki a Darfur dake yammacin kasar Sudan, inda jaridar Rheinischer Merkur take batu a game da wani mataki na rashin imani da kisan kare dangi irin shigen wanda ‘yan Hutu suka dauka a kasar Ruwanda misalin shekaru goma da suka wuce, Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Shin nahiyar Afurka tana fuskantar barazanar sake fadawa ne a cikin wani bala’i na kisan kare dangi irin shigen wanda ya wakana a kasar Ruwanda shekaru goma da suka wuce? Akwai dai dalilai masu yawa dake yin nuni da haka. Domin kuwa matakan tsaftace kabila da Larabawa jajayyen fatu ke dauka akan ‘yan uwansu Musulmi bakar fata a Darfur dake yammacin Sudan daidai yake da wanda dakarun sa kai na Impuzamugambi na kabilar Hutu suka dauka akan ‘yan Tutsi a shekarar 1994. An fatattki dubban daruruwan mutane daga yankunansu na asali a yammacin Sudan. A cikin watan afrilun da ya gabata, a lokacin juyayin samun shekaru goma da wanzuwar ta’asar ta Ruwanda, sakatare-janar na MDD Kofi Annan yayi kiran daukar nagartattun matakai domin kandagarkin duk wani mataki na kisan kare dangi da ka taso. Kuma ko da yake an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, amma har yau dakarun sa kai na Larabawa na ci gaba da kai farmaki kan bakar fata da kokarin farautar wadanda suka tsere zuwa kasar Chadi.

Ita kuwa jaridar Die Zeit ta bayyana takaicinta ne a game da sako-sako da kungiyoyi na kasa da kasa ke yi a game da rikicin Darfur, inda ta kara da cewar:

"Muddin ba tura askarawan kiyaye zaman lafiya aka yi zuwa yankin Darfur dake yammacin Sudan ba yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tamkar magana ce ta fatar baka kawai. Alkaluma na MDD sun nuna cewar a halin yanzu haka an fatattaki mutane sama da miliyan daya daga gidajensu, wanda ya kama kwatankwacin kashi daya bisa biyar na illahirin mazauna lardin. Da yawa daga wadannan ‘yan gudun hijira an tsugunar da su ne a wasu sansanonin da dakarun sa kai na Larabawa ke da ikon kai musu farmaki a cikin gadin gaba. Sama da mutane dubu dari suka nemi mafaka a kasar Chadi kuma ba su da ikon samun cikakken taimako na jinkai."

A wannan makon MDD tayi Allah Waddai da abin da ta kira matakan ta’addanci na gwamnati a kasar Cote d’Ivoire. A lokacin da take bayani game da haka jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

"A cikin rahoton da ta gabatarwa da MDD wata tawagar bincike da majalisar ta nada domin bitar kisan gillar da aka yi wa mutane kimanin 120 lokacin zanga-zanga a Abidjan watan maris da ya wuce ta dora wa gwamnatin kasar Cote d’Ivoire laifin wannan ta’asa. Wannan mataki da sojoji da ‘yan sanda suka dauka ya kara tsaurara barakar dake akwai tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye da kuma barazanar tabbatar da rarrabuwar kasar ta yammacin Afurka gida biyu."

A cikin wata sabuwa kuma shugaba Mugabe na Zimbabwe ya lashi takobin saka wando daya da masu karbar hanci a tsakanin jami’an siyasar kasar. To sai dai kuma wannan matakin ya fi shafar masu kananan alhaki ne a cewar jaridar Die Tageszeitung, wacce ta kara da cewar:

"Wasu majiyoyi amintattun sun ce matakin yaki da cin hanci da shugaba Mugabe ya gabatar ya shafi wasu mutane ne 500, wadanda suka hada da jami’an siyasa da ‘yan kasuwa da kuma ma’aikata na kungiyoyi masu zaman kansu, da ake zargi da laifuka na cin hanci da kuma cinikin kudaden musaya da albarkatun kasa ba a bisa ka’ida ba. Amma fa in har Mugabe da gaske yake yi to kuwa wajibi ne ya fara daga kan mukarrabansa dake cin karensu ba babbaka tare da wawashe dukiyar kasar Zimbabwe.

To madalla. Masu sauraro da wannan muke kammala rahotannin na jaridun Jamus akan al’amuran Afurka sai kuma in ce Zainab gareki.