A Thailand an koma gidan jiya | Labarai | DW | 30.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Thailand an koma gidan jiya

An sami fashewar bom a Bangkok na kasar Thailand inda mutane suka sami rauni

default

Tashin hankali a Bangkok

Rahotanin daga ƙasar Thailand sun ce da alama an koma ga samun ɓarkewar tashe tashen hankula a birnin Bankok, bayan da wani bam din yaa fashe a tsakiyar garin wanda ya hadasa mumunar rauni ga wani mutuman

Hukumar 'yan sanda ta ƙasar ta shaida cewa bam din, a naɗe shi ne a cikin wata jaka kuma aka ajiyeta a kusa da wata shara a wata unguwar da ke kusa da gine gine gwamnatin a daidai lokacin da ake samun yawan kai da kawo na jama'a

Tun a cikin watan Afrilu ne dai gwamnatin ƙasar ta kafa dokar ta baci, a duk faɗin ƙasar a sakamakon zanga zangar 'yan adawar ta nuna ƙin jinin gwamnatin da aka ƙwashe makonni ana yi, wace a cikinta mutane 90 suka mutu yayin da wasu 2000 suka jikata

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane

Edita: Umaru Aliyu