1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A ranar talata za´a gana tsakanin Abbas da Blair a Ramallah

Yunkurin da gwamnatin gaggawa ta Falasdinu karkashin jagorancin FM Salam Fayyad ta yi na a tabbatar da ita a majalisar dokoki ya citura. Majalisar dokokin dai ta kasa yin zama a yau saboda da rashin isassun wakilai da suka hallara a majalisar a yau. A wani labarin kuma kuma sabon wakilin samar da zaman lafiya a GTT Tony Blair zai yi ganawarsa ta farko da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a ranar talata mai zuwa. Babban mai shiga tsakani na Falasdinu Saeb Erekat ya ce za´a yi ganawar ne a hedkwatar Abbas da ke birnin Ramallah na gabar yamma da kogin Jordan. A baya an yi ganawa da dama tsakanin Abbas da Tony Blair a lokacin da yake rike da mukamin FM Birtaniya. Blair zai kuma tattauna da shugabannin Isra´ila a wata ziyarar yini biyu da zai fara a yankin a gobe litinin.