A ranar talata za´a gana a Makka tsakanin Abbas da Mashal | Labarai | DW | 04.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A ranar talata za´a gana a Makka tsakanin Abbas da Mashal

Shugaban Falasdinawa kuma jagoran kungiyar Fatah Mahmud Abbas zai gana da shugaban Hamas dake gudun hijira Khaled Mashal a birnin Makka a ranar talata mai zuwa. Hakan ya zo ne sakamakon yarjeniyoyin tsagaita wuta da sassan biyu ke karyawa da kuma tashe tashen hankulan a Zirin Gaza da Gabar Yammamcin Kogin Jordan da suka yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 28 tun daga ranar alhamis. Sarki Abdullah na Saudiya ke karbar bakoncin tattaunawar da za´a yi da zumar sasanta kungiyoyin Hamas da Fatah da ba sa ga maciji da juna. Shi ma FM Falasdinawa Isma´il Haniya na shirin halartar taron, kamar yadda jami´ai a ofishin sa suka nunar.