A ranar 26 ga watan yuli za´a yi kuri´ar raba gardama a Falasdinu | Labarai | DW | 10.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A ranar 26 ga watan yuli za´a yi kuri´ar raba gardama a Falasdinu

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya sanar cewa a ranar 26 ga watan yuli za´a gudanar da kuri´ar raba gardama akan kafa wata kasar Falasdinu mai makwabtaka da Isra´ila, a wani mataki na warware rikicin yankin GTT. A yau dai ne hukumar mulklin cin gashin kan Falasdinu ta bayyana haka a birnin Ramallah. An dai mba da wannan sanarwa ce duk da adawar da kungiyar Hamas mai jan ragamar mulki, ke nunawa da ´yancin wanzuwar kasar Isra´ila. Tuni dai Hamas ta yi kira da a akuracewa kuri´ar raba gardamar. Batun da za´a kada kuri´ar a kai shi ne ko Falasdinawa zasu so kafa wata kasarsu a cikin iyakokin 1967 wato bayan yakin da aka gwabza da Isra´ila. Wannan batun kuwa tamkar amincewa da wanzuwar Isra´ila ce. Masu lura da al´amuran yau da kullum sun yi hasashen cewa Abbas zai samu rinjaye na masu goyon bayan matsayin sa na wanzuwar kasashen biyu.