A ranar 17 ga watan nuwamba za´a gudanar zaɓe a Kosovo | Labarai | DW | 01.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A ranar 17 ga watan nuwamba za´a gudanar zaɓe a Kosovo

A ranar 17 ga watan nuwamba mai zuwa masu kada kuri´a a lardin Kosovo dake cikin Sabiya zasu gudanar zabukan kananan hukumomi da na majalisar dokoki. Kantoman MDD a wannan lardin mai rinjayen kabilar Albaniya, Joachim Rücker ya ba da wannan sanarwa bayan wani taro da yayi shugaban Kosovo da kuma FM a birnin Pristina, hedkwatar lardin. Ko da yake ana ci-gaba da tattaunawa a birnin Vienna a dangane da makomar Kosovo, amma har yanzu sassan biyu na nesa da cimma wata yarjejeniya. Yayin da Alabaniyawan Kosovo ke neman ´yancin kai daga Sabiya, ita kuwa gwamnatin Belgrade cewa ta yi ba zata taba barin wannan yanki ba. a kuma halin da ake ciki Faransa ta karbi jan ragamar dakarun kiyaye zaman lafiya na KFOR daga Jamus. Ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung na daga cikin mayan bakin da suka halarci bukin a birnin Pristina.