1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Nijar an kulla kawancen 'yan adawa

Abdoulaye Mamane Amadou/USUApril 19, 2016

Jami'an bangarorin biyu sun yi haka ne a wani mataki na sake dabarar yakar gwamnatin shugaba Isoufou da suka kira mai sarawa inda ba gaba

https://p.dw.com/p/1IYWm
Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Koda yake ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance suna da ma irin babbar alkiblar da sabon kawancen zai sakawa gaba ba, wata majiya kwakkwara dai ta tabbatarwa tashar DW cewar kusan an kammala duk wasu shirye-shiryen da suka cancanta. Inda za su dauko daga 'yan adawa har izuwa ga wasu kungiyoyin na farar hula da na kwadago, domin kafa wani sabon kawancen da 'yan adawa suka kira, shi ne mafi a’ala wajan sake sabon salon yin fito na fito da gwamnatin, a ciki da waje ta hanyar sabon kwancen da ke tafe da sabon salo irin na gwagwarmaya.

To ko bayyanar wannan sabon kawancen na nufin kenan kawancen COPA2016 da 'yan adawar suka kafa kasa da watanni uku ya sha ruwa kenan? Tambayar kenan da wakilin DW ya yi wa Tidjani Abdoulkadri, sakataren jam’iyyar MNSD Nasara mai adawa.

Yace "Babban makasudin yin COPA shi ne na yin zabubbuka koda yake zabubbukan da muka fadi, ba’ayi su a cikin ka’ida ba to amma ai yanzu batun zaben ya riga ya kare kenan, wata sabuwar kokuwa ce kenan. Doli muma kanmu mu sake salo don ganin cewar, wasu sabbin abukanen tafiya sun shigo mu sake fadada wannan sabon gungun, ya kasance kowa yana nan yanayi ne ya sake. Saboda ba’a taba zabubukan da aka yi irin wadan nan ba"

Duk da yake ba’a kai ga fayyace manufofinsa ba a bayyane take da cewar sabon kawancen na da gurin ne sake maido da martabar 'yan adawan biyo bayan nuna alamar zubewarta a idon wasu magoya baya, ta hanyar matakin da suka dauka a baya musamman ma kan aminta da shiga majalisa da komawa hukumar zabe da ma yarda da tafiya zaben kananan hukumomi.

Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta