A Nigeria jamián tsaro na sintiri domin kwantar da tarzoma. | Labarai | DW | 25.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Nigeria jamián tsaro na sintiri domin kwantar da tarzoma.

A Nigeria jamían tsaro na cigaba da sintiri a manyan biranen kasar inda aka sami tashe tashen hankula a rikicin addini da ya barke tsakanin musulmi da mabiya addinin Kirista wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 157 a fadin kasar. Dauki ba dadi tsakanin mabiya addinan biyu ya haifar da damuwa a kasar ta Nigeria, kasa mafi yawan alúma a nahiyahar Afrika. Kasar dai ta sami kann ta a cikin wani mawuyacin hali inda a hannu guda take fama da ƙaruwar hare haren yan takife akan cibiyoyin mai a yankin Niger Delta, a daya hannun kuma ga annobar cutar masassarar tsuntsaye da ta bulla a kasar. A yanzu dai hukumomin Nigeriar sun umarci sarakunan gargajiya da shugabannin addini a fadin kasar da su sanya baki domin kwantar da hankulan alúmomi da kuma magoya bayan su. Manazarta alámuran yau da kullum na baiyana cewa rigingimu a game da makomar siyasar kasar da kuma batun tazarcen shugaban kasar Olusegun Obasanjo tare da wasu gwamnonin jihohi na kara haifar da rarrabuwar kawuna a yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe a shekara mai zuwa.