A na ci-gaba da tashe tashen hankula a birnin Mogadishu
May 13, 2006Talla
A yau asabar wani kazamin fada ya sake barkewa a Mogadishu babban birnin Somalia kwanaki bakwai a jere a daidai lokacin da mayakan musulmi da madugan yaki ke fafatawa don karbe iko a birnin. Yanzu haka dai yawan wadanda suka rasu sakamakon fadan baya-bayan nan ya kai mutum 140 yayin da wasu daruruwa suka jikata. Mazauna birnin na kokarin tserewa zuwa yankunan birnin da ba´a tashin hankali a cikinsu to amma daukacin su kan ratsa tsakanin masu rikicin. Ana ci-gaba da wannan fada duk da kiran da kasashen duniya suka yi na a kwantar da hankali, bayan wani tayin tsagaita bude wuta da manyan malaman islama suka yi. Kawancen madugan yakin dai sun yi fatali da wannan tayi.