1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A na ci gaba da lugguden wuta tsakanin Isra´ila da Hezbollah

August 3, 2006
https://p.dw.com/p/Buo4

A na ci gaba da ɓarin wuta tsakanin dakarun Isra´ila da na yan Hebollah a kudancin Labanon.

Tsakanin daren jiya zuwa sahiyar yau, Isra´ila, ta kai ƙarin hare haren bama- bamai a sassa dasdama na Labanon, to saidai Hezbollah, na ci gaba da turjewa ta ban mamaki.

Ya zuwa yanzu,rundunar tsaronTshal, ta jibge dakaru fiye da dubu 10 a kudancin Labanon, to amma sun kasa cimma burin Praminista Ehud Olmert, na kakkaɓe mayaƙan Hizbullahi, wanda su ma ke ci gaba da tsilla rokoki zuwa Isra´ila.

A sahiyar yau ma, sun harba a ƙalla guda 20 masu dogon zango.

A jawabin da ya gabatar jiya, Praministan Ehud Olmert ya ce Isra´ila zata ci gaba da kai hare haren, har lokacin da Majalisar Dinkin Dunia,, ta aika rundunar shiga tsakani.

To saidai har yanzu, babu wanda ke da masaniya a kann lokacin aika wannan runduna, ta la´akari da ja in jar da a ke fama da ita tsakankin membobin komitin Sulhu a kan batun.

A sakamakon hakan ne, ƙungiyar hadin kan musulmi ta dunia,OIC, a zaman taro na mussamman da ta shirya, a ƙasar Malaisia,ta yi suka da kakkausar halshe, ga Majalisar Ɗinkin Dunia, da manyan ƙasashen dunia, da ta ke zargi da nuna san rai, a rikici tsakanin Isra´ila da Hizbollahi.

A cikin jawabin da ya gabatar, sakatare Jannar na ƙungiyar OIC, ya bayana ɓacin ran musulmi,a dangane da halin ko in kulla, da mayan ƙasashen dunia ke nunawa a game da luggudan wutar da Isra´ila ke zubawa, a Labanon, wanda ya zuwa, ya hadasa assara rayukan kussan 900 na al´ummomi fara hulla.