A na ci gaba da gwabzawa tsakanin dakarun NATO da yan taliban | Labarai | DW | 31.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A na ci gaba da gwabzawa tsakanin dakarun NATO da yan taliban

A ƙasar Afghanistan, ana ci gaba da fafatawa, tsakain dakarun tsaro na NATO, da yan taliban.

A sahiyar yau, 2 daga sojojin ƙasa da ƙasa, su ka rasa rayuka , a yayin da wasu ƙarin 2 su ka ji mumuna raunuka, sakamakon tarwatsewar wata Bom, a yankin Nuristan da ke kussan iyaka, da Pakistan.

Hukumomin, Afghanistan sun zargi makwaciyar su Pakistan, da bada talafi ga mayakan Taliban.

Daga farkon shekara da mu ke ciki, zuwa yanzu, sojojin rundunar ƙasa da ƙasa 115, su ka sheƙa lahira a wannan yanki.

Yan taliban da Amurikawa su ka kora, daga karagar mulki a shekara ta 2001, sun alƙawarta fatatakar sojojin mamaya.