A na ci-gaba da gangamin kayar da gwamnatin Siniora a Libanon | Labarai | DW | 04.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A na ci-gaba da gangamin kayar da gwamnatin Siniora a Libanon

An halaka mutum daya a wani artabu da aka yi tsakanin magoya bayan Syria da wasu kungiyoyi dake adawa da Syria a Libanon. Kamar yadda ´yan sanda suka shaidar wasu mutane da dama sun samu rauni lokacin da wata mota dauke da tutar kungiyar Hisbollah ta afkawa wani gungun mutane a wata unguwa ta birnin Beirut. A wannan unguwar ce aka yiwa tsohon FM Libanon Rafik Hariri da wasu mutane kisan gilla a cikin watan fabrairun shekara ta 2005. a jiya lahadi ma wasu dubban mutane suka yi gangami na neman FM Fuad Siniora da yayi murabus. Sai dai FM ya ce ba zai saduda da matsin lamba daga masu zanga-zangar da ke goyon bayan Hisbollah.