1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A karon farko tun bayan kawo karshen yakin Iraki, an kashe wani Bajamushe a wannan kasa.

Kamar yadda kafofin yada labarun Jamus a birnin Bagadaza suka nunar, an kashe wani injiniya Bajamushe da kuma takwaransa dan kasar Holland a wani hari da aka kai musu a kusa da birnin Kerbela. Ga kasar ta Holland wannan shine karon farko da ta rasa wani dan kasar a Iraqi, a ta bakin wata mai magana da yawun ma´aikatar huldar da kasashen waje a birnin The Hague.

Rahotannin da suka iso mana daga birnin Bagadaza sun ce baya ga injiniyoyin biyu, an kuma halaka direbansu dan Iraqi da kuma wani dan sandan kasar. Rahotannin sun kara da cewa mutanen hudu na kan hanya ne zuwa birnin Bagadaza lokacin da wasu ´yan bindiga da ba´a gane su ba, suka budewa motarsu wuta da manyan bindigogin masu aman harsasai. Wani kakakin sojin Amirka ya tabbatar da faruwar wannan danyan aikin to amma bai yi karin bayani ba.

Yankin da abin ya faru dai yana hannun kulawar sojojin kasar Poland ne a kudu da babban birnin Iraqi. Kuma jim kadan bayan an kai harin sojojin Poland sun yiwa yankin kofar rago, to amma ba´a gane wadanda suka kai harin ba, inji wadanda suka shaida abin da ya faru da idanunsu.

Injiniyoyin dai na yiwa wani kamfanin birnin Bremen aiki ne. Wannan kamfanin dai shi ke aikin gyara wuraren tsabtace ruwa a birnin Kerbela da kewaye, amma ya zuwa yanzu ba´a san wanda ya ba shi kwangilar yin wannan aiki ba. Bayan kisan da aka yiwa wasu Amirkawa 4 ´yan kungiyar wani coci a birnin Mosul dake arewacin Iraki a ran litinin da ta wuce, masu lura da al´umaran daka je ya komo ke fargabar cewa ´yan takife a Iraki zasu yawaita kaiwa fararen hula na ketare hare-hare.

A fili ya ke cewa ´yan takife a wannan kasa sun kuduri aniyar kai hare-hare akan fararen hula na kasar, wadanda ke yiwa gwamnatin rikon kwarya ko kuma hukumar mulkin Amirka Iraki aiki ko kuma suke ba su hadin kai. Su dai ´yan takifen na adawa da ko-wane irin yunkuri na samar da zaman lafiya a wannan kasa, saboda haka suka juya akalar wannan aika-aika da suke yi akan kamfanonin Turai da kungiyoyin ba da agaji wadanda ke ba da gudummawa don ganin zaman lafiya da kwaciyar hankali sun wanzu cikin kasar.

Alkalumman da ma´aikatar harkokin wajen Jamus ta bayar sun yi nuni da cewa akwai Jamusawa kimanin 50 dake zama na dindindin a Iraki. Baya ga haka kuma sai ´yan kasuwa na Jamus wadanda ke yawaita kai ziyara wannan kasa da nufin kulla huldodin kasuwanci a Iraki.

Manazarta al´amuran yau da kullum sun nuna fargabar cewa harin na jiya talata zai sa ´yan kasuwan Jamus su rika yin takatsantsan game da tafiya zuwa Iraki. Alal misali ana iya dakatar da ziyarar da wata tawagar ´yan kasuwar Jamus ke shirin kaiwa birnin Bagadaza cikin watan gobe, don halartar wani bikin baje koli da nufin sake gina Iraki.

A kullum dai daukacin ´yan Iraki ko dai ´yan siyasa ko kamfanoni ko kuma talakawa suna maraba da kamfanonin Jamus a wannan kasa.

 • Kwanan wata 17.03.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlF
 • Kwanan wata 17.03.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlF