1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A karon farko mata sun shiga zaɓe a ƙasar Koweit

June 29, 2006
https://p.dw.com/p/BusM

Yau ne a ƙasar Koweit, a karo na farko, ake gudanar da zaɓen yan majalisun dokoki, wanda ya samu halartar yaya mata, a matyayi yan takara, da kuma damar kaɗa kuri´a.

Shekara 1 ,bayan samu wannan yanci, na zaɓen yaya mata, 28 sun ajje takara, daga jimmilar yan takara 249.

Saidai da dama daga cikin su, sun yi ƙorafin fuskantar barazanar a lokacin yaƙin neman zaɓe, dalili da hakan, wata daga cikin su ta janye takara da ta ajje.

A na gudanar da zaɓen na yau, a sakamakon wata baddaƙƙala da ta kunno kai, tsakanin gwamnati da majalisar Dokokin ƙasar, wada a sakamakon ta, Sarki Scheik Sabah al Ahmad al sabah, ya rushe majalisar dokoki, ranar 21 ga watan mayu da ya wuce.

Yan takara jama´iyun adawa, sun zargin takwarorin su masu riƙe da ragamnar mulki, da sayen ƙuri´un jama´a.

A jimilce, mutane dubu 340 ne, ya cencenta su ka kaɗa ƙuri´a a fadin ƙasar baki ɗaya, wanda kashi 57 bisa 100 mata ne.

A na sa ran, fara samun sakamakon zaben,tun daga daren yau alhamis.