1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A karo na farko, shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni ya tattauna da ƙungiyar ’yan tawayen LRA da ke yaƙan gwamnatin ƙasar.

December 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuYJ

A karo na farko tun shekaru 20 da suka wuce, shugaba Yoweri Museveni na ƙasar Uganda ya tattauna kai tsaye da shugabannin ƙungiyar ’yan tawayen LRA na ƙasar. Rahotanni sun ce shugaba Museveni, ya shafe minti 30 yana tattaunawa kan wayar tarho da Vincent Otti, muƙaddashin shugaban ƙungiyar LRA ɗin, wanda ya bayyana masa cewa duk da shawarwarin zaman lafiyar da ɓangarorin biyu ke yi, har ila yau sojojin gwamnatin Ugandan na yi wa wasu sansanonin ’yan tawayen ƙawanya.

A cikin wata fira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Reuters, Martin Ojul, shugaban tawagar ƙungiyar ’yan tawayen, a shawarwarin zaman lafiyar da ake gudanarwa a kudancin Sudan, ya ce wannan tattaunawar da shugabannin ɓangarorin biyu suka yi dai na nuna irin muhimmancin da ita ƙungiyar LRA ɗin ke bai wa yunƙurin da ake yi ne na samad da zaman lafiya.