A kalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunan bakin wake da aka kai a birnin Bagadaza. | Labarai | DW | 01.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A kalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunan bakin wake da aka kai a birnin Bagadaza.

Rahotannin da ke iso mana daga birnin Bagadaza, sun ce a kalla mutane 8 ne suka sheka lahira, yayin da wani dan harin kunan bakin wake ya ta da bam a tsakiyar birnin Bagadaza da sanyin safiyar yau. Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta bayar na nuna cewa, a kalla mutane 30 ne kuma suka ji rauni.

Harin ya wakana ne a unguwar Baab al-Sharjee, inda jama’a ke taruwa don neman aiki.

`Yan yakin gwagwarmayar Iraqin dai na iza wuta ne a yunkurin da suke yi na hambare gwamnatin kasar. Kawo yanzu dai, sun halaka dimbin yawan jami’an tsaro da kuma fararen hula a hare-haren da suke ta kaiwa a duk fadin kasar.