1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A kalla mutane 12 sun rasa rayukansu sakamakon tashin nakiya a wani sansanin sojin Rasha a yankin Checheniya.

February 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8v

Kafofin yada labaran kasar Rasha da kuma wasu majiyoyin soojin kasar, sun ruwaito cewa, a kalla mutane 12 suka rasa rayukansu, sa’annan wasu 28 kuma suka ji rauni, yayin da nakiya ta tashi a wani sansanin sojin Rashan da kwe Checheniya. Har ila yau dai, ba a san dalilin da ya janyo tashin nakiyar ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Rashan nan RIA-Novosti, ta ari bakin shugaban ma’aikatar kula da ayyukan agaji na gaggawa a yankin, Kanar Akhmet Djeirkhanov, yana mai cewa.

An dai kafa wani kwamiti don ya binciko ko kuma ya farauto wadanda ka iya aikata laifin ta da bamabaman, yayin da ma’aikatan ceto kuma ke ta nemo wadanda suka tsira daga tarkacen gine-ginen da nakiyar ta rusa. Wata majiyar `yan sandan yankin ta ce, ana zaton bututun gas da ke kicin na karkashin daya daga cikin gine-ginen ne ya fashe, ya kuma janyo annobar. Sai dai, har ila yau jami’ai sun ce bas u ga wata alamar fashewar bututun ba.