1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A jiya lahadi dai a kalla Amerikawa 18 ne suka bakunci lahira a wani yakin sunkuru da yan kasar suka gudanar a jiya a yankin fallujah

A cikin wannan yamutsin kuwa a kalla dakarun Amurka 16 ne suka mutu a yayin da aka kakkabo jirginsu a sararin samaniyar yankin tare da samun raunika ga wasu dakarun 20 .Wannan dai ya kasance farmaki mafi muni tun bayan da aka kawo kashen yakin da aka gwabza da Sadam a watan Maris na wannan shekara tare da kawo karshen Gwamnatinsa a watan Afrilun wannan shekarar da muke ciki .A sanyin safiyar nan ta yau ne sauran dakarun da suka damu mummnunan raunika a ka kawo su nan jamus domin magani a wani Asibiti a Ramstein barikin Sojin Amurkan dake nan jamus .Tun bayan mulkin Sadam dai a kalla an kashe sama da dakaru n Amurka 250 cikin yamutsin dake rutsawa da dakarun a wani kwantan bauna da yan kasar kerwa DaKARUN BATARE DA KAKKAUTAWA BA :A BISA HALIN RAYUWA DAI A CAN KASAR TA IRAQ A YANZU YAWANCIN MAAIKATAN KASA DA KASA SUN FARA FICEWA DAGA KASAR TARE DA KUNGIYOYIN SA KAI a HANNU GUDA KUKA WANI FARAMAKIN A DAREN JIYA YAYI SANADIYAAR MUTUWAR FARAREN HULA HUDU A YANKIN Kirkuk a tsakanin bangarorin biyu .Haka zalika wani yaro ya fada wannan tarkon inda ya rasu bayan da ya fadfa hannun bangarorin biyu a yankin fallujah a jiya A yau kuma wani Bom ya fashe a lardin baquba inda ya hallaka dan kasar Iraq daya tare da raunata wasdu mutane biyu .To sai dai duk da wannan yamutsi da jkasar ta fada a ciki shugaba Bush na Amurka yace ba gudu ba kuma ja da baya a dangane da manufofin kasar amurka kann iraq ..Yace ficewar dakarun Amurka a kasar a yanzu haka tamkar bayar da wata dama ce ga yan taasdda domin su cikarensu babu babbaka ..To sai dai har kawo yanzu yaki ya ambata komai kann kakkabo jirgin Amurkan da akayi a jiya lahadi .Babu shakka wannan batun dai ya haifar da kace nace a tsakaninnAmerikawan na dalilan da suka sanya jiragen saman Amurka ke ratsawa wannan yankin dake da hatsarin gaske a halin yanzu .WAta majiya dai tace shugaba bush na Amurka ya sake fadawa wani tarkon mai wuyar fita bisa halin da dakarun kasar ke cikin a iraq .