A daina katsalandan a rikicin Dafur inji Gaddafi | Labarai | DW | 29.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A daina katsalandan a rikicin Dafur inji Gaddafi

Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi ya ja hankalin kasashen yammacin turai a game da yin katsalandan a rikicin yankin Dafur na kasar Sudan yana mai jaddada adawa da tura sojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa. Gaddafi yace ba zai yiwa gamaiyar kasa da kasa dadi ba suka rika tsoma baki a cikin alámuran da wani bangare na kasar baya bukata ba. Ya yi wannan kalamin ne yayin da yake jawabi ga jakadun kasa da kasa a birnin Sirte dake kusa da Tripoli. Jakadun wadanda suka hada dana Majalisar dinkin duniya da kungiyar gamaiyar Afrika da Amurka da kuma na wasu kasashen yammacin turai sun tattauna ne a game da rikicin Dafur da kuma yadda zaá yiwa tufkar hanci. Jakadan Amurka a Sudan Jan Eliasson yace matsalar Dafur bama kawai yana da hadari bane ga Sudan har ma da duniya baki daya. A waje guda kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun gudanar da zanga zangar lumana a kasashe da dama na duniya ta zagayowar shekaru hudu da rikicin Dafur.domin jawo hankalin duniya su taimaka waje kawo zaman lafiya a Dafur.