A cikin wata jaridar Isra′ila, an buga wani shafin talla, | Siyasa | DW | 03.11.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A cikin wata jaridar Isra'ila, an buga wani shafin talla,

inda kamfanin da ya sayi wannan shafin ya ce yana bukatar mata, wadanda za su iya bari a dasa musu dan tayi, wanda aka sarrafa a kwalba, a cikinsu, har zuwa lokacin da za su haihu. Idan sun haifi yaran kuma, sai kamfanin ya biya su, wato matan, sa'annan ya karbi `ya`yan. A cikin wannan tallar dai an kuma bayyana cewa, an fi son matan da suke huskantar karancin kudi wajen biyan bukatun halin rayuwarsu na yau da kullum. Irin yawan matan da suka amsa wannan tayin, ya bai wa kamfanin da ya sa tallan ma mamaki.
Amma a kashin gaskiya, babu wannan kamfanin. Wata kungiyar kare hakkin mata ta Isra'ilan, mai suna Na'amat ce, ta bad da kammani ta sanya wannan tallar a jaridar. Dalilin yin haka kuwa shi ne janyo hankullan mahukuntan kasar kan irin mummunan halin da iyalai da yawa ke ta kara samun kansu a ciki, musamman ma dai matan da ke renon `ya`yansu su kadai da kuma ma'aurata matasa. Shugaban wannan kungiyar, wata lauya mai suna Talia Livne ta bayyana cewa:-
"Mun sanya wannan tallar a jarida ne don jawo hankalin gwamnatin Isra'ila kan matsalar da ta janyo wa al'ummanta. Gwamnatin ba ta nuna wata sha'awar tallafa wa matasa don su iya aure su kuma haifi `ya`ya. Wannan tallar dai na hasashe ne kan yadda al'umman Isra'ila za ta iya kasancewa, a cikin `yan shekaru masu zuwa nan gaba, bayan mun yi ta samun koma baya har mu kai ga matsayin kasashe masu tasowa. Muun sami dai amsoshi da yawa, inda matan ke bayyana mana cewa, wannan ita kadai ce mafitar da suke gani za ta iya taimakansu wajen kula da `ya`yansu".
Chanan da Limor Ochajun, daga kauyen Batyam kusa da Tel Aviv, na cikin iyalai matalauta na wannan sabon salon. Suna da yara uku, amma uwar, Limor, ita kadai ce mai aiki a wani kanti, inda albashinta na wata kuma bai wuce Euro dari 7 ba. Dukkansu kuma sun dogara ne kacokan kan wannan albashin. Tun daga farkon wannan wata ne aka sallami mijinta Chanan daga gun aikinsa. Daga wannan lokacin dai, Limor ta bayyana cewa:-
"Ba na iya barci kuma. Duk safiya tun wajen karfe hudu nake farkawa in yi ta tunanin, yadda za mu iya ci gaba da tafiyad da harkokin rayuwanmu, yadda za mu iya biyan haraji, da kudin wutar lantarki, da kudin gidanmu. Akwai ababa da yawa da ba za mu iya biya wa kanmu ba kuma."
A halin yanzu dai, an katse wa Limor tarhon dinta, kuma a cikin `yan makwanni masu zuwa ma, ba za ta iya kallon talabijin ba kuma. Ta dai bayyana cewa, babu abin da take fargaba kamar ta rasa gidan da suke ciki, idan suka gaza biyan banki kudin da suke biya wata wata a kan gidan.


 • Kwanan wata 03.11.2003
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvnp
 • Kwanan wata 03.11.2003
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvnp