1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A cikin doki da murna dubban Falasdinawa sun tsallake kan iyakar Rafah

November 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvJJ

Sama da Falasdinawa dubu 2 ne suka tsallaka kan iyakar Rafah dake tsakanin Zirin Gaza da kasar Masar a yau asabar kwana daya bayan bude kan iyakar a hukumance. A karon farko tun bayamn shekarar 1967, Falasdinawa sun tsallake kan iyakar ba tare da fuskantar wani binciken na jami´an tsaron Isra´ila ba. Yanzu haka dai hukumomin Falasdinawa ke iko da iyakar a karkashin kulawar jami´an KTT EU. Daukacin Falasdinawa miliyan 1.3 dake zaune a Gaza ba su taba tasallake kan iyakar mai tsawon kilomita 40 ba. Za´a rika bude kan iyakar tsawon sa´o´i 4 a kowace rana har asai dukkan jami´an sa ido na kungiyar EU sun isa can a tsakiyar watan desamba.