1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A bude taron koli na Kungiyar ECOWAS

January 12, 2006
https://p.dw.com/p/BvCd

An bude taron koli na Kungiyar Tattalin arzikin kasashe 15 na Afrika ta yamma ECOWAS a birnin Niamey na jamhuriyar Nijar,inda ake sa ran taron zai maida hankali akan tsaron yankin.

Sai shugabannin kasashe 5 ne kadai suka halarci taron,sauran kasashen sun turo firaministocinsu ko kuma ministocin harkokin wajensu domin su wakilce su.

Shugabannin Najeriya,Togo Mali,Guinea Bissau da mai karbar bakunci na Jmahuriyar Nijar suka halarci bude taron.

Taron na yau ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar take murnar samun nasarar gudanar da zabe a kasar Liberia da kuma kafa gwamnatin wucin gadi a kasar Ivory Coast,wadda ta rabe gida biyu tun 2002.

Shugabannin zasu maida hankalin tattunawar ce akan rahoton da ministocin harkokin wajen kungiyar suka hada a makon da ya gabata game da tsaro da kwanciyar hankalin yankin.

Hakazalika zasu tattauna ci gaba da aka samu kawo yanzu wajen kafa rundunar dakarun wucin gadi 6,500 na kungiyar cikin shirye shiryen tsaro na Tungiyar Taraiyar Afrika.