1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A an sami sakamakon zaben da aka gudanar a jiya a nan jamus

Bayan kada kuruu a jihar NRW a nan jamus alkaluma sun nunar da cewa an kusan kunnen doki a tsakanin manyan jamiyyun siyasar kasar

A lokacin kada kuria a daya daga cikin runfunan zaben

A lokacin kada kuria a daya daga cikin runfunan zaben

zaben dai ya nunar da cewa da kwance uwa kwance akayi a tsakanin manyan jamiyyun siyasar kasar ta SPD da CDU a jihar ta NRW jihar data fi kowace jiha girma a nan kasar ta jamus .sai dai kuma duk da wannan koma baya jamiyyar spd da shugaban gwambnati jamus Gerhard schroeder ya nuna farin ciki da yarda jamiyyar ta samu karin masoya idan aka kwatanta ta da sakamakon zaben data samu a shekara ta 1999.Kamar dai yarda jaridar Tages zaietung ta ruwaito cewa sakamakon zaben dai ya nunar da cewa jamiyyar cdu ta adawa ta gaza samun kurun data samu a shekara ta 1999 a yayin da jamiyyar dake mulki ta spd ta sami kaso 31.9 a wannnan zaben wanda a wancan zaben shekara ta 1999 ta sami kaso 33.9.Jamiyyar adawa ta cdu ta sami klaso 43.4 a wannan zaben wanda ta gaza samun kaso 50.3 a sakamakon zaben da aka gudanar a shekara ta 1999.To sai dai jamiyyar da cdu ta sami nasara a wannan zabe kuma tana cike da murna da farin ciki a halin yanzu ..To sai dai a hannu guda jamiyyar schroeder ta spd na cike da karsashi bisa sakamakon wannan zabe wanda zai kasance tamkar wani mizani ne na zaben yayan majalisar dokoki da zaa gudanar a watan mayun shekara mai kamawa idan allah ya kaimu .Kamar dai yarda shugaban jamiyyar spd na kasa Franz Muentefering yace sakamakon wannan zabe ba wai na nuna karsashi bane a halin yanzu illa karin kaimi na cimma gaci a zaben da zaa gudanar a nan gaba a fadin kasar baki daya ..Yace a yanzu yana cike da murna da farinciki bisa sakamakon wannan zabe fiye da yarda yake ciki a makonni kusan bakwai da suka gabata .Idan dai baa mantaba a zaben yayan majalisar hukumar zartarwar kungiyar gamaiyar turai da aka gudanar a watan yunin wannan shekara jamiyyar ta spd tasha kaye wanda a halin yanzu ke hannunka mai sanda a dangane da sakamakon wancan zabe da aka gudanar a nan jamus da kuma sauran kasashen turai baki daya .Bugu da kari a zabubbukan da aka gudanar a cikin wannan kasar musamman a gabashinta jamiyyar dake mulki ta sha kashi .Ga misali a jihohin Saarland Saxany da Brandenburg .Wannan kuwa baya rasa nasaba da gazawar gwamnatin kasar ne na shawo kann rashin aikinyi ga jammaar kasar musamman matasa .A dangane da haka ne kuwa gwamnatin kasar ke samun sakamako a runfunan zabe wanda tuni yan kasar ke kosawa a dangane da sauye sauyen da gwamnati keyi a halin yanzu .Shugabar jamiyyar adawa ta cdu Angela Markel tace sakamakon zaben ya nunar a fili cewa rinjaye ake bukata ba soki burutsu ba wanda jamiyyar cdu tayi fice a sakamakon wannan zaben na yan watannin nan a fadin kasar baki daya .

 • Kwanan wata 27.09.2004
 • Mawallafi Mansour bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvgA
 • Kwanan wata 27.09.2004
 • Mawallafi Mansour bala Bello
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvgA