1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Amurka yan majalisar wakilai sun amince da sabon shirin kiwon lafiya

' Yan majalisar wakilai na ƙasar Amurka sun ƙaɗa Kuri´a amincewa da sabon shirin kiwon lafiya da shugaba Barack Obama ya gabatar.

default

Shugaba Barick Obama na Amurka

  A Amurka ´yan majalisar wakilai sun  ƙaɗa  ƙuria 'a amincewa da daftarin ƙudirin da gwamnatin shugaba Barack Obama ta gabatarmasu da shi akan shirin samar da inshora ga al´uma. Kaɗa ƙuria' wanda akansa a ka shafe kusan awowi goma ana ta tabka zazzafa mahawara, tsakanin  yan jam'iyar Demokrate da Republicain masu adawa, a ƙarshe ´yan majalisar 219 suka amince da shirin yayin da 212 suka ƙaɗa ƙuria' Ƙin amincewa. Shekaru kusan ɗari ,gwamnatocin da suka shuɗe a ciki hada Theodore Roosvelt da Bill Clinton sun sha faman cimma ɓurin ganin a amince da dokar amma ba tare da sun samu nassara ba.

Wani bincikken da aka gudanar a shekara ta 2007 ya nuna cewa a ƙasar ta Amurka kowane mutun ɗaya na kashe  a ƙalla dalla Amurka 7290 na kiwon lafiya abinda ke zaman sama ga dalla 3000 ga ƙasashen Nowe dakuma Suizerland.Da yake mayar da martanin domin godiya ga yan majalisar na wakilai Obama ya ce duk da matsalar tattalin arzikin dake da akwai bai kaucewa aƙidarsa ba,sannan ya fuskanci ƙalubale wanda kuma ya cimma nassara a kansa.

A wannan nasara da shugaba Obama ya samu,dake zaman tarihi a ƙasar, masu lura da al amura na hasashen cewa zata ƙara masa martaba dakuma kwarjini.

Wannan sabon tsari dai na kiwon lafiya ana sa ran  zai shafi kishi 95 cikin ɗari na yawan al umar ta Amurka a ƙalla yan shekaru 65,a kwai da miliyoyin Amerikawan dake da inshora ta saye wace bata biya masu ɓukata akan sha'anin kiwon lafiya, ga ƙasar da kula da kiwon lafiya ke da tsananin tsada fiye da ƙasahen Jamus, da Faransa,dakuma Suizerland.

Mawallafi Abdourahamane Hassane Edita Yahuza Sadissou