A Ƙasar China an kashe wani ɗan fasaƙoɓri na miagun kwayoyi | Labarai | DW | 06.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Ƙasar China an kashe wani ɗan fasaƙoɓri na miagun kwayoyi

Mahukumta a ƙasar China sun kashe wani ɗan ƙasar japan da aka samu da laifin fatauci miyagun kwayoyi

default

Sojojin ƙasar China na sintiri

An bada rahoton cewa an kashe wani ɗan fasa ƙoɓri na miyagun kwayoyi ɗan ƙasar Japan a arewa maso gabacin ƙasar china, mutumen mai sunan Mitsunobu Akano ɗan shekaru 65 wanda ya kamata a kashe tun a jiya litinin an jinkirta domin ya samu damar ganawa da iyalensa.

wanan kisa dai shine na farko da ƙasar ta China ta aiwatar akan wani baƙo ɗan ƙasar Japan tun da aka sake ƙula hulɗa diflomasiya tsakanin ƙasashen biyu shekaru 38 da suka wuce, friministan ƙasar Japan Yukio Hatoyama ya bayyana takaicinsa akan yadda ya ce hukumcin ya yi tsauri,to amma ya sheda cewar ƙasar sa bata da yancin yin katsa london a cikin harakokin sharia'a na wata Ƙasa.

Hukumomin dai na ƙasar ta China sun ce nan gaba a ranar alhamis mai zuwa za a zartas da irin wannan hukumcin kisan ga wasu mutane kuma guda ukku yan ƙasar ta Japan a China waɗanda suma aka samesu da laifin fatauci miyagun kwayoyin

Mawallafi: Abdourahamane Hassane.

Edita :Abdullahi Tanko Bala