Aƙalla mutane 64 sun rasu a wani hari da aka kai kan jirgin ƙasa a Indiya | Labarai | DW | 19.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aƙalla mutane 64 sun rasu a wani hari da aka kai kan jirgin ƙasa a Indiya

Fiye da mutane 64 sun rasu sannan wasu da ba´a san adadin su ba sun jikata a wani harin bam da aka kai kan wani jirgin kasa dake kan hanya daga jihar Haryana dake arewacin Indiya zuwa kasar Pakistan. Daukacin wadanda harin ya rutsa da su ´yan Pakistan ne. Ministan sufurin jiragen kasa Lalu Prasad ya ce an dana bama-baman ne a cikin taragu biyu na jirgin. Ministan ya ce da hannun masu matsanancin kishin Islama a harin, wanda ya ce wani yunkuri ne na yiwa shirin zaman lafiya tsakanin Indiya da Pakistan yankan baya. A cikin kwanaki masu ake sa ran isar ministan harkokin wajen Pakistan Mian Khursheed Mahmud Kasuri a Indiya, inda zai tattauna da takwaransa na wannan kasa.