Ɗaurin talala ga Aung San Suu Kyi | Siyasa | DW | 11.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ɗaurin talala ga Aung San Suu Kyi

Wata kotun soja a birnin Rangun na ƙasar Bama ta yankewa Aung San Suu Kyi hukunci ɗaurin talala da watanni 18.

default

Aung San Suu Kyi ta shiga saban ɗaurin talala

A yau ne wata kotu dake birnin Rangun na ƙasar Bama ta yanke hukunci ɗaurin talala na watani 18 ga madugun ´yan adawar ƙasar Aung San Suu Kyi.

Ƙasashen duniya na cigaba da maida martani agame da hukunci da suka danganta na rashin adalci.

Da farko, kotin sojojin ƙasar Bama, ta yanke hukunci ɗaurin shekaru uku a kurkuku, tare da aikin badala ga Aung San Suu Kyi, kafin daga bisani a sassabto hunkunci, zuwa ɗaurin talala na watani 18, kamar yadda wani kakakin gwamnati ya nunar:Kotu ta kama Aung San Suu Kyi, da mutane da tayi haɗuwar siri da su a gidanta a lefin cin amanar ƙasa.Saboda haka, ta yanke masu hukuncin shekaru uku a gidan yari.Amma bisa umurnin shugaban ƙasa Janar Than Schwe, an sassabto hukunci zuwa wazani 18.Kuma zata zama a gidanta ta na damar kalon talbajan ta karanta jaridu, kokuma ta je asibiti.Amma ga masu bukatar ziyarartar sai sun samu izini daga gwamnati.

A cewar Pavin Chachavalpunpong wani masani ta fannin harakokin ƙasa da ƙasa, gwamnatin Bama ta ɗauki wani mataki domin rage kaifin martanin ƙasashen duniya: Wannan matakin sassauci da gwamnati ta ɗauka tayi, shine domin auna martanin ƙasashen duniya.A taƙaice Aung San Suu Kyi, ta zama tamkar ƙadagaran bakin tulu ga gwamnatin Bama.

To saidai ganin cewar "ature bata raba kare da kura", tunni ƙasashe duniya sun fara yi Allah wadai ga hukunci, wanda suka danganta da tsabar rashin adalci.

Haɗin gwiwar mutane 14 da suka ta samun tukwicin Nobel a ƙasashe dabamdabam na duniya, sun fido wata sanarwa, inda suka yi kira ga Majalisar Ɗinki Duniya, ta gudanar da bincike a ƙasar Bama tare da zargin hukumomin ƙasar da aikata kisan kiyasu da take haƙƙoƙin jama´a.

A nata ɓangare, Sakatariyar harakokin Amirka Hillary Clinton dake cigaba da ziyara aiki a Afrika ta bayana takaici ga hunkuci sannan ta bukaci gwamnmatin mulkin sojan ƙasar Bama, ta sako firsinoni fiye da 2000 wanda a halin yanzu ke tsare a kurkuku, ba tare da hujja ba.

A ɗaya wajen, Hillary Clinton, ta bayana wajibcin tattanawa tsakanin ´yan adawa da ƙabili dabam dabam, wanda shine sharaɗin da Amirka ta gitta kamin zaɓen da ƙasar zata shirya baɗi.

Su kuwa ƙasashen Faransa da Italiya, sun buƙaci Ƙungiyar Tarayya Turai ta fiddo matakin bai ɗaya, domin ladabtar da gwamnatin muklin sojan ƙasar Bama a game da abinda ƙasashen suka danganta da ɗanyan hukunci da ta yankewa Aung San Suu kyi .

kakakin ´yan adwar ƙasar Bama dake gudun hijira Soe Aung, kira yayi ga ƙasashe duniya tare da cewar ɗauki mataki na zahiri ga hukumomin Bama:Wannan hukunci da aka yankewa Aung San Suu Kyi, abin takaici ne. A ciki da wajen Bama jama´a tayi Allah wadai da shi.Gwamnati tayi kunen uwar shegu ,ga kiranye-kiranyen da ake mata.Saboda haka lokaci yayi ƙasashe duniya su ɗauki matakin mai ƙarfi, a maimakon sabbatu na fatar baka.

Tun dai shekara ta 2007 ƙungiyar Tarayyar Turai ta saka takunkumi sayar da makamai ga ƙasar Bama , tare da haramtawa magabatan ƙasar shiga ƙasashen EU, da kuma saka takunkumi ga kuɗaɗen da suka mallaka a bankunan ƙasahen Tarayya Turai.

Mawallafi:Musch-Borowska/Yahouza

Edita: Abdullahi Tanko Bala