Ɗan takarar ´yan adawa a Saliyo ke kan gaba a zaben ƙasar | Labarai | DW | 10.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɗan takarar ´yan adawa a Saliyo ke kan gaba a zaben ƙasar

Rahotanni daga Saliyo sun ce dan takarar jam´iyar adawaa zagaye na biyu na zaben shugabn kasar da aka gudanar a karshen mako Ernest Koroma yana kan gaba a yawan kuri´un da aka kidaya kawo yanzu. Sakamakon da ba na hukuma daga mazabu sama da kashi daya cikin 3 ya yi nuni da cewa dan takarar na jam´iyar All People´s Congress, Koroma ya samu kashi 54 cikin 100 yayin da mataimakin shugaban kasa mai barin gado Solomon Berewa ya ke da kashi 45 cikin 100. To sai dai magoya bayan Berewa sun yi ikirarin cewa dan takarar su ne ke kan gaba. Sai dai nan da kwanaki masu zuwa ne ake sa ran samun sakamakon karshe na zaben.