Ɗan kunar bakin wake a Afghanistan ya halaka mutane 27 | Labarai | DW | 10.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɗan kunar bakin wake a Afghanistan ya halaka mutane 27

Akalla mutane 27 sun rasu sannan wasu da dama suka samu raunuka lokacin da wani dan kunar bakin wake a kasar Afghanistan ya ta da bam a jikin shi. Jami´ai sun ce an kai harin ne a garin Gershk dake lardin Helmand na kudancin kasar. Dan kunar bakin wake dai yana kan babur ne kuma bisa ga dukkan alamu ´yan sanda ya yi niyar kaiwa harin. Jami´an ´yan sanda da dama na daga cikin wadanda wannan ta´asa ta rutsa da su. Lardin Helmand ya kasance wani dandalin gwabza fadace fadace mafi muni a kasar tsakanin dakarun da NATO ke yiwa jagora da kuma ´yan tawayen Taliban.