1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɗan asalin Pakistan ake zargi da harin New-York

Hukumomin Amirka sun kama wanda ake zargi da kai harin ranar asabar a birnin New-York.

default

Dandalin shaƙatawa na Times Square

Hukumomin Amirka sun tsafke wani ɗan asalin ƙasar Pakistan da ake zargi da yunƙurin kai hari kan dandalin shaƙatawa nan na Times Square da ke birnin New-York a ranar asabar da ta gabata.

Ministan shari´a na ƙasar ta Amirka, wato Eric Holder ya ce an kama wani matashi mai suna Shahzad Faisal a filin jirgin sama a lokacin da ya ke neman arcewa daga ƙasar i zuwa Dubai. Wannan matashi mai shekaru 30 da haihuwa, yana da zama ne a jihar Connecticut na arewa maso gabashin Amirka.

Tun a jiya ne hukumomin  na Amirka suka fara farautan wanda ake zargi da yunƙurin ɗana bam a cikin wata mota ruwa a jallo. Ba akai ga samun alaƙa da ƙungiyar Taliban ta ƙasar Pakistan da ta yi iƙirarin kai harin da kuma shi Faisal da aka kama ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu