Ɓarkewar kwalera a Nigeria | Labarai | DW | 17.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓarkewar kwalera a Nigeria

Cutar amai da gudawa ta haddasa mutuwar mutane 87 a arewacin Nigeria daga cikin 1315 da suka kamu da ita.

default

Masu fama da amai da gudawa

Cutar amai da gudawa da ta ɓarke a Nigeria na ci gaba da yaɗuwa a wasu jihohin arewacin ƙasar, tare da haifar da salwantar rayukan mutane da dama. Kawo yanzu dai aƙalla mutane 87 suka rigamu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar da rashin tsabtar muhalli da kuma ruwa mai tsafta ke haddasawa.

A jihar Bauchi mutane 47 cutar ta kwalara ta ritsa da su, yayin da wasu ƙarin 1200 ke fama da ita. A jihar Borno kuwa mutane 40 aka tabbatar cewa sun kwanta dama, yayin da wasu ƙrin 115 ke kwance a sansanonin da hukumomi suka keɓ domin kula da masu fama da cutar ta amai da gudawa.

Wannan dai ba shi karon farko da ake fiskantar ɓarkewar cutar ta kwalara a arewacin Nigeria ba. Ko a watannin farko na shekarar da ta gabata, sai da mutane 260 suka rasa rayukansu biyowa bayan kamuwa da cutar ta amai da gudawa da suka yi.

Mawallafi:Mouhamadou Awal

Edita:Zainab Mohammed Abubakar