Ɓarin wuta tsakanin dakarun NATO da yan Taliban a Afghanistan | Labarai | DW | 21.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓarin wuta tsakanin dakarun NATO da yan Taliban a Afghanistan

Fiye da mutane 20 su ka rasa rayuka a sabuwar bata kashin da ta haɗa dakarun rundunar ƙasa da ƙasa a Afghanistan da mayaƙan Taliban.

A cewar wata majiyar rundunar yan sandar Afghanistan, wanda su ka mutun sun haɗa da yan taliban19 da kuma jami´an tsaro 2.

Rikici mafi muni ya faru a yankin Ghazni, inda yan taliban ke ci gaba da yin garkuwa da mutunanen Korea ta Kudu 19, da kuma bajamishe ɗaya.

A cen ma yankin Helmand a na ci gaba da gwabza faɗa tsakanin ɓangarorin 2.

Tun makon da ya gabata ne, rundunar ƙungiyar tsaro ta NATO ta ƙaddamar da wani gagaramin hari, da zumar murƙushe yan taliban a wannan yankuna , to saidai ya zuwa yanzu, su na fuskantar turjiya ta ban mamaki daga dakarun Taliban.

A cewar Egon Bahr, babban jami´i ,mai kulla da hulɗoɗi da ƙasashen ƙetare na jam´iyar SPD a nan Jamus, samar da kwanciyar hankali mai ɗorewa a ƙasar Afghanistan na buƙatar ƙarin sojojin ƙasa da ƙasa masu yawa.