Ɓarin wuta a Mogadiscio tsakanin dakarun kotunan Islama da sojojin gwamnati | Labarai | DW | 29.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓarin wuta a Mogadiscio tsakanin dakarun kotunan Islama da sojojin gwamnati

A birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia, a na ci gaba da ɓarin wuta, tsakanin mayaƙan sunƙuru, da dakarun gwamnati, masu sami goyan baya, daga ƙasar Ethiopia.

A tsukin kwanaki 2 da su ka wuce, ɓangarorin 2, sun yi faɗa mai muni, wanda ya sa dubunan mutane su ka ƙauracewa wannan birni.

A jiya lahadi, ɗaruruwan mazauna Mogadiscio, sun shirya zanga-zangar ƙin jinnin sojojin Ethiopia.

Sannan sojojin sun yi harbin kann mai uwa da wabi, wanda ya hadasa mutuwar mutane a ƙalla 3, tare da jima da dama raunuka.

A ɓangaren siyasa kuwa, a na ci gaba da taƙwan sako tsakanin shugaban ƙasa Abdullahi Yusf Ahmed, da paraminista Ali Mohamed Gedi.

A wani jawabi da ya gabatar jiya gaban yan majalisa, shugaban ƙasa ya buƙaci su tsige Praminista.