1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓarin wuta a Libanon

A ƙasar Libanon A na ci gaba da ɓarin wuta tsakanin dakarun gwamnati da ƙungiyar yan takife ta Fatah Al-Islam.

A ɗaya hannun kuma wata kotu a birnin Beyruth ta gurfanar da mutane 20 membobin wannan ƙungiya,tare da zargin su da hadasa fitina cikin ƙasa.

Ƙungiyar Fatah Al Islam ta yi watsi da kiran gwamnati na tasgaita wuta.

ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa, sun bayyana matuƙar damuwa, a game da matsalolin da su ke fuskanta, wajen kai agaji ga al´ummomin yankin Nahr Al Bared, wanda a halin yanzu ke cikin halin buƙata a sakamakon faɗan da ya ɓarke, a wannan matsugunin yan gudun hijira.