1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ɓaraka tsakanin Amirka da Isra'ila

Ɓaraka tsakanin Amirka da Isra'ila tana ƙara girma

default

Hillary Clinton

Alamun ɓaraka tsakanin Amirka da Isra'ila sai ƙara fitowa a fili suke yi. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta ce sanarwar gina sabbin mutsugunan Yahudawa 1,600 a gabashin birnin Ƙudus da Isra'ila ta mamaye, wanda aka yi dai lokacin da mataimakin shugaban ƙasar Amirka Joe Biden yake yankin, wani cin fiska ne ga Amirka a faɗar Clinton. Sakatariyar harkokin wajen Amirka wadda ta ɗauki mintuna 43 tana caccakar matakin da firayim ministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya ɗauka, ba da safai akan ji irinsa daga bakin wani jami'in gwamnatin Amirka ba. Su ma dai Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai da ƙasar Rasha duk sun yi Allah wadai da wannan matakin, wanda suka ce taƙala ne, kana kuma wani babban tarnaƙi ne ga zaman lafiya.

Mawallafi: Shehu Usman

Edita Mohammad Nasiru Awal