1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ɓaraka a cikin jam´iyar ANC

Shirye shirye sun kankama a ƙoƙarin kafa wata ƙungiya da za ta yi hannun riga da jam´iyar ANC mai jan ragamar mulki a Afirka Ta Kudu.

default

Shugaban ANC Jacob Zuma

To sai dai masharhanta sun ce dole sai wannan sabuwar jam´iya ta ƙunshi shugabanni masu kishin ƙasa kafin ta yi nasara.


Tsohon ministan tsaron Afirka ta Kudu Mosiuoa Lekota wanda kuma na hannun damar tsohon shugaban ƙasa Thabo Mbeki ne ya nunar a jiya Laraba cewa a cikin makonni ƙalilan masu za a kafa wata jam´iya da za ta ɓalle daga ANC.

Ya ce: "Ko shakka babu game da gaskiyar cewa ba za mu taɓa yarda a rusa mulkin demoƙuraɗiyya a Afirka Ta Kudu ba. Saboda idan ba mu gamsu da abubuwan dake wakana ba, dole mu ɗauki matakin yin wani abu daban. A gareni ya zama wajibi mu kasance cikin wata ƙungyia daban."

Lekota wanda ake yiwa laƙabi da ɗan ta´adda, ya yi murabus daga majalisar ministoci bayan da ANC ta tilastawa shugaba Mbeki yin murabus a watan da ya gabata. Ya ƙaddamar da wata yekuwar sukar lamrin jam´iyar wadda ta jagoranci yaƙi da mulkin nuna wariya a Afirka ta Kudu. An yi imanin cewa Lekota na samun goyon baya daga masu biyayya da Mbeki waɗanda suka fusata sakamakon matakin da jam´iyar ta ɗauka na tilasta masa sauka watanni ƙalilan gabanin cikar wa´adin muƙaminsa. To sai dai kawo yanzu ba ɗaya daga cikin fitattun ´yan siyasar ƙasar da nuna goyon bayan shirin kafa sabuwar jam´iyar. Lekota ya ce za su yi wani taro na ƙasa cikin makonni masu zuwa inda za su bayyana shirinsu a fili.


Ya ce: "Muna adawa da masu fatali da kyawawan manufofin ANC. Na yi imani da akwai wasu ƙusoshin ANC waɗanda ba sa jin daɗin abubuwan dake faruwa. Shi ya sa ina ganin yau tamkar mun gabatar da takardun neman saki ne."

Masharhanta a ƙasar sun ce dole sai sabuwar jam´iyar wadda Lekota ya lashi takobin kafawa ta ƙunshi shugabannin na ƙwarai da ake mutuntasu idan ta na son ta yi nasara kuma ta samu goyon bayan masu kaɗa ƙuri´a a zaɓukan dake tafe a ƙasar.

Wasu tsofaffin shugabannin ´yan gwagwarmaya kamar Archbishop Bishop Desmond Tutu da Dr. Alan Boesak sun fito fili sun yi tir da fatali da manufofin ANC da ake yi, wanda suka ce dubban rayuka sun salwanta domin girke su. Mista Tutu ya ma ce ba zai kaɗa ƙuri´a a zaben mai zwua ba.

A halin da ake ciki shugaban ANC Jacob Zuma da wasu manyan jami´ansa na ƙokarin kwantar da hankulan jama´a.

Ya ce:"Babu ɓaraka a cikin jam´iyar kamar yadda wasu ke faɗi. Muna aiwatar da manufofi ne na demoƙuraɗiyya. Wasu sun yi ma hasashen cewa ANC za ta rushe. Hakan ba mai yiwuwa ba ne."


Yanzu haka dai ɓangaren Zuma sun ce za su nemi Mbeki ya yiwa ANC kamfen a zaɓe mai zuwa to sai dai masharhanta na siyasa sun ce da wuya Mbeki ya amsa wannan kira.

Sauti da bidiyo akan labarin