ƙura ta laffa a birnin N´djamena na ƙasar Tchad a yaki tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati | Siyasa | DW | 13.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ƙura ta laffa a birnin N´djamena na ƙasar Tchad a yaki tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati

Shugaba Idriss Deby na Tchad ya bayyana cewar sojoji masu biyyaya ga gwamnati sun murƙushe yan tawaye.

default

A tsukin yan kwanaki 2 da su ka gabata, yan tawayen FUC, sun matsa ƙaimi, na sai sun kiffar da shugaba mai ci yanzu, Idriss Deby Itno, da ya share shekaru da dama bisa karagar mulkin ƙasar.

A yammacin jiya, rahotani sun bayyana cewar, yan tawayen FUC, na kussa da shiga birninN´Djamena, sannan yau da sahe, da dama daga ayarin su, sun abkawa birnin, inda dakaru masu biyyaya ga gwamnatai su ka taka masu birki, bayan sa´o´i ,ana amen wuta.

Shugaba Idriss Deby, a wata hira da yayi, da gidan Redion France, ya ce a halin yanzu, dakarun gwamnati ke riƙe da babban birnin, saidai kakakin yan tawaye a France, tsofan ministan harakokin wajenTchad,ya ce su ke riƙe da kashi 80 bisa 100, na ƙasar.

A halin da a ke ciki dai, rahotani daga birnin N´Djamena sunce ƙura ta laffa.

Sannan jiragen sama, masu durra angullu, tare da taimakon rundunar ƙasar France na ci gaba, da shawagi, a sararin samaniyar birnin.

Ƙasar France, na da dakaru 1.200 a Tchad, sannan an ƙara tura wata rundunar France, da ta ƙunshi sojoji 150.

Shaidu daga birnin N´Djamena sunce, sojojin ƙasar France ne, su ka ceci rundunar shugaba Idriss Deby a sahiyar yau, ta fannin luggudan wuta, ga yan tawaye.

Shima kakakin yan tawayen a ƙasar France, Laona Gong, ya ce sojojin France sun yi amen wuta, a biranen Adre, da Mudeina, kussa da iyakar ƙasar Sudan, biranen da halin yanzu, ke cikin hannun yan tawaye.

Opishin jikadancin France, a N´Djamena, ya mussanta wannan zargi.

Saidai, ya tabattar da cewa, sojojin France sun yi harbi, don yin tsawa, ga yan tawaye a hanyar su, ta shiga N´Djamena, da zumar garkuwa ga Fransawa, da ke wannan birni.

Kuma wannan harbi, bai kashe ko ɗan tsako ba.

Nan gaba a yau ne, hukumar tsaro ta ƙungiyar Tarayya Afrika, zata zaman taro, na mussaman, a Addis Ababa, domin tunani, a kan wannan matsala da Tchad ke fuskanta.

Hausawa kann ce, ba farau ba ke da ciwo ramau, domin shima Idriss Deby Itno, shugaba mai ci yanzu, ya hau karagar mulkin bayan ya kiffar da shugaba Hissein Habre.

Shugaba Deby,na zargin gwamnatin ƙasar Sudan da tallafawa yan tawayen Tchadi, domin gudanar da juyin mulki.

Wata ƙungiyar tawaye, ta yankin Darfur, ta gasganta, wannan zargi.

Ahmed Hussain, kakakin wannan ƙungiya, ya ce ko shakka babu, yan tawayen Tchad, na samun tallafin kayan aiki, da kuɗaɗe, da hussa´o´in yaƙi daga gwamnatin ƙasar Sudan.

 • Kwanan wata 13.04.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0d
 • Kwanan wata 13.04.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0d